Isa ga babban shafi

MDD ta bukaci gwamnatin sojin Mali ta sako sojojin Ivory Coast

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci kasar Mali da ta sako wasu sojojin Ivory Coast 46 da ake tsare da su, bayan da gwamnatin sojin kasar ta soki kalaman babban sakataren MDD Antonio Guterres, kan rikicin na tsawon watanni biyu.

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteres.
Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteres. REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya a cikin wata sanarwa da ya fitar ya nuna matukar damuwa tare da kira da a gaggauta sakin sojojin Ivory Coast da ake tsare da su.

Sanarwar ta ce tana goyon bayan duk wani kokarin da ake yi na sako wadannan sojojin, tare da maido gyara kyakkyawar alakar makwabtaka a tsakanin kasashen biyu.

Ivory Coast ta ce an tsare sojojin ne a ranar 10 ga watan Yuli a filin tashi da saukar jiragen sama na Bamako, yayin da suke kokarin taimakawa rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya MINUSMA.

Gwamnatin sojin Mali ta dage kan cewa, sojojin da ta kama na haya da ke neman yiwa kasarta kutse.

Guterres, a wata hira da ya yi da RFI a baya-bayan nan, ya ce a bayyane yake sojojin ba na haya ba ne, lamarin da ya sa firaministan kasar Mali da aka nada, Kanar Abdoulaye Maiga, ya yi suka ga babban jami’in Majalisar Dinkin Duniya a jawabinsa da ya gabatar a babban taron Majalisar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.