Liverpool ta koma ta daya a saman teburin gasar Firimiyar Ingila
A daren Alhamis ne kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta lallasa Sheffield United da ci 3 da 1 a filin wasanta (Anfield).
Wallafawa ranar:
Tun da farko Dan wasan Liverpool Dan kasar Uriguy Darwin Nunez ne ya zura kwallo daya a ragar Sheffield United a minti na 17.
Sai dai daga bisani bayan dawowa daga hukutun rabin lokaci Conor Bradley Dan yankin Arewacin Ireland kuma Dan wasan Liverpool ya zura kwallo guda a ragar kungiyarsa, (own goal).
A minti na 76 Dan kasar Argentina kuma Dan kwallon tsakiya a kungiyar ta Liverpool Alexis Mac Allister ya kara kwallo ta biyu a ragar Sheffield United, yayin da Dan wasa Cody Hakpo ya cike kwallo ta 3 a ragar Sheffield united din a minti 90.
Wannan nasara ce ta bawa Liverpool damar darewa saman teburin gasar da maki 70, yayin da Arsenal ke biye mata da maki 68, sai ta 3 a saman teburin gasar Manchester City da ke da maki 67, dukkan su kuma sun buga wasanni 30-30 a gasar.
Yanzu haka dai kungiyar Sheffiend United ita ce a mataki na karshe da maki 15 kuma a ranar 4 ga watan gobe ne na Mayu za su fafata da Nottingham Forest ta 17 a teburin gasar Premier da a yanzu haka ta ke da maki 25.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu