Isa ga babban shafi

Dortmund da Atletico sun kai matakin kwata final a gasar zakarun Turai

A daren jiya Laraba ne aka kammala wasannin zagaye na biyu na gasar zakarun Turai, inda a yanzu aka samu kungiyoyi 8 da suka kai matakin dab da na kusa da na karshe a gasar ta bana.

Yadda dan wasa Jadon Sancho na Borussia Dortmund da sauran 'yan wasan kungiyar ke murna bayan jefa kwallo a ragar PSV a gasar zakarun Turai.
Yadda dan wasa Jadon Sancho na Borussia Dortmund da sauran 'yan wasan kungiyar ke murna bayan jefa kwallo a ragar PSV a gasar zakarun Turai. REUTERS - Thilo Schmuelgen
Talla

A wasannin da aka yi a daren Laraba, Borussia Dortmund ta samu nasara akan PSV da ci biyu da nema, kuma ta samu nasarar ce bayan kwallayen da Jadon Sancho da kuma Marco Reus suka jefa mata, lamarin da ya bai wa Dortmund damar kai wa mataki na gaba a gasar ganin ta jefawa jumullar kwallaye 3 a dukkanin wasanni biyu da suka yi, yayin da PSV ta jefa kwallo daya tilo.

A dayan wasan kuwa, Atletico Madrid ce ta yi waje road da Inter Milan a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Yadda 'yan wasan Atletico Madrid suke murna bayan da da suka fidda Inter Milan daga gasar zakarun Turai.
Yadda 'yan wasan Atletico Madrid suke murna bayan da da suka fidda Inter Milan daga gasar zakarun Turai. REUTERS - Violeta Santos Moura

Atletico Madrid ce ta samu nasara a wasan bayan da aka tashi ci biyu da daya, sai dai duk da nasarar da ta samu sai da aka buga bugun daga kai sai mai tsaron gida, domin dukkanin kungiyoyin na da kwallaye biyu a ragar juna a dukkanin wasanni biyu da suka yi.

Da wannan nasara, a yanzu kungiyoyi 8 da suka samu nasarar tsallaka wa zagayen dab da na kusa dana karshe a gasar zakarun Turai sun hada da Arsenal da Barcelona da Bayern Munich da Atletico Madrid da kuma Borussia Dortmund.

A gobe Juma’a ne kuma za a hada yadda wadannan kungiyoyi za su kara da juma a wannan zagaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.