Isa ga babban shafi

Liverpool ta ci gaba da jagorancin teburi bayan doke Luton da kwallo 4 da 1

Liverpool ta doke Luton da kwallaye 4 da 1 a haduwarsu ta daren jiya Laraba nasarar da ta bata damar kara tazarar da ta ke da ita a jagorancin teburin Firimiya zuwa maki 4.

Mai tsaron baya na Liverpool Virgil van Dijk.
Mai tsaron baya na Liverpool Virgil van Dijk. POOL/AFP
Talla

Tun farko Luton ta zura kwallo a minti na 12 da fara wasa ta hannun Chiedozie Ogbene kuma har zuwa tafiya hutun rabin lokaci Reds ba ta iya ta farke ba, ka zalika kwallon ta Ogbene ita ke matsayin karon farko da Luton ke zura kwallo a ragar Liverpool a Anfield tun bayan shekarar 1992.

Halin da aka shiga a farkon wasan na jiya dai ya sanya fargabar yiwuwar tawagar ta Luton town wadda wannan ne karon farko da ta ke dawowa Firimiya cikin kusan shekaru 30 ta iya nasara a Anfield.

Kafin tafiya hutun rabin lokacin Liverpool ta shiga tsaka mai wuya musamman bayan da damarmaki suka rika kufcewa Luis Diaz.

Sai dai bayan dawowa daga hutun rabin lokacin Virgil van Dijk ya budewa tawagar ta Jurgen Klopp da kwallon farko a minti na 56 gabanin Cody Gakbo ya kara wata a kasa da mintuna 2 tsakani.  

Luis Diaz ya zura kwallo ta 3 a minti na 71 kana Harvey Elliott ya kara wata a minti na 90, wasan da ke matsayin karo na 15 da Luton ke fita daga Anfield ba tare da samun maki ba.

Karawar ta jiya ke matsayin wasa na 100 da Elliott ya dokawa Liverpool haka zalika wasa na 3 a jere da tawagar ke nasara tun bayan shan kayenta a hannun Arsenal da kwallaye 3 da 1 cikin watan jiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.