Liverpool ta karbi jagorancin teburin Firimiya bayan doke Burnley
Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta koma jagorancin teburin Firimiyar Ingila bayan doke Burnley da kwallaye 2 da nema a haduwarsu ta daren jiya Talata.
Wallafawa ranar:
Kwallayen wanda Reds ta samu ta hannun ‘yan wasa Darwin Nunez a minti na 6 da fara wasa da kuma Diago Jota a minti na 90 gab da tashi daga wasa sun baiwa tawagar ta Jurgen Klopp damar kara yawan makinta zuwa 42 banbancin maki 2 tsakaninta da Arsenal wadda ke da wasa guda a hannu.
Wasan wanda ya gudana a gidan Burnley Liverpool ta samu nasarar ne duk da soke kwallon Harvey Elliot wadda ya ci da taimakon Mohamed Salah bayan da rafali ya bayyana ta a matsayin ta satar fage.
Liverpool na fuskantar kalubale daga Arsenal wadda kje Shirin haduwa da West Ham a gobe Alhamis, wanda matukar ta yi nasara a karawar kenan dole Reds ta koma matsayin ta 2.
Kafin haduwar ta jiya dai Burnley na matsayin ta 17 ne a teburin na Firimiya yayinda bayan rashin nasarar ta jiya kai tsaye ta koma ta 19.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu