Isa ga babban shafi

Da yiwuwar a kammala cinikin Manchester Uniteed kafin Kirsimeti

Da yiwuwar a karkare dambarwar cefanar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United kafin nan da ranar 25 ga watan nan na Disamba bayan da Sir Jim Ratcliffe ya nanata cewa a kage ya ke kamfaninsa na Ineaos Group ya biya fam biliyan 1 da miliyan 250 don sayen kashi 25 na kungiyar.

Babban filin wasan Manchester United.
Babban filin wasan Manchester United. © AFP / OLI SCARFF
Talla

Fiye da shekara guda kenan da Iyalan gidan Glazer suka bayyana aniyar sayar da kungiyar ta Manchester United, sai dai bayan doguwar tattaunawa tun daga wancan lokaci har zuwa yanzu an gaza daidaitawa game da tayin Ratcliffe.

A yau juma’a ne za a yi haduwa ta musamman da wakilan bangarorin biyu wato bangare masu saye da masu sayarwa kuma matukar aka cimma jituwa kai tsaye Ratcliffe zai zama mai rike da kashi 1 bisa 4 na hannun jarin kungiyar.

Ko a watan Oktoban da ya gabata dai an ga yadda Sheikh Jassim bin Hamad Al Thani attajirin Qatar ya janye daga shirin sayen United bayan kin amincewa da fam biliyan 5.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.