Isa ga babban shafi

Carabao: Liverpool da Fulham, Chelsea da Middlesbrough za su kara a Semi-finals

Liverpool za ta kara da Fulham yayin da Chelsea za ta kara da Middlesbrough a wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin Carabao.

Kofin gasar kwallon kafar Carabao
Kofin gasar kwallon kafar Carabao © reuters
Talla

Tawagar Jurgen Klopp ta lallasa West Ham da ci 5-1 a yammacin Laraba, inda ta kai zagayen ‘yan hudu na karshe, yayin da Fulham ta samu bugun daga kai sai mai tsaron gida a Everton a ranar Talata.

Chelsea

Ita ma Chelsea ta doke Newcastle a bugun fanariti a wasan daf da na kusa da na karshe, yayin da Middlesbrough ta yi nasara da ci 3-0 a kan Port Vale ta mamaita wasan karshe na 1998.

Za a doka wasannin biyu ne a ranakun 8 da 22 ga watan Janairu na shekarar 2024 mai kamawa.

Da wannan mataki Liverpool ta kai wasan karshe na 14 a tarihinta inda ta yi nasara sau 10 a gasar da ta fara lashe wa a shekarar 1981.

Fulham

Fulham ta Marco Silva, wacce ta je Anfield a haduwar farko, rabonta ta buga wasan kusa da na karshe a makamaicin irin wanna gasa, tun a shekarar 2010, lokacin da ta kai wasan karshe a gasar cin kofin Europa.

Middlesbrough

A halin da ake ciki kuma, kungiyar Boro da ke Championship, wacce ta karbi bakuncin Chelsea a haduwarsu ta farko, a karon farko Kenan ta kai matakin kusa da na karshe tun shekarar 2004, lokacin da ta lashe gasar ta dauki babban kofi daya tilo.

Chelsea, wacce ta lashe gasar cin kofin FA a 1997 da kuma na karshe a gasar cin kofin League shekara guda bayan ta doke Teessiders, tana neman lashe gasar a karo na shida tare da karbar kyautar farko tun bayan da ta ci gasar cin kofin duniya na kungiyoyin a 2021 da aka jinkirta zuwa Fabrairun shekarar da ta gabata.

An shirya buga wasan karshe a filin wasa na Wembley ranar Lahadi 25 ga watan Fabrairu.

Wasan kusa da na karshe na Kofin EFL:

Liverpool da Fulham

Middlesbrough da Chelsea

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.