Girona ta koma saman teburin Laliga bayan doke Alaves
Kungiyar kwallon kafa ta Girona, wadda ke bada mamaki a gasar Laligar Spain ta koma saman teburin Laligar bayan lallasa Alaves da ci 3 da nema a daren Litinin.
Wallafawa ranar:
Artem Dovbyk ne ya fara saka kwallo a raga bayan da mai tsaron ragar Alaves, Antonio Sivera ya ture kwallon da Yan Couto ya buga masa.
Couto, wanda Girona ta dauko aro daga Manchester City ya samu bugun daga-kai-sai-mai tsaron raga, kuma dan wasan tawagar kasar Ukraine, Dovbyk ya buga ya ci kwallonsa ta 10 a gasar wannan kaka.
Dovbyk ne dan wasan da ya fi tsada a kungiyar, bayan da saye shi a kan kudi fam miliyan 6 daga Dnipro a kakar da ta gabata.
Yanzu Girona na kan gaba a gasar Laliga, inda tazarar maki biyu ne tsakanin ta da Real Madrid, wadda ke a matsayyi na biyu a gasar.
Kungiyar Girona, wadda ke yankin Catalan, kuma ba ta taba lashe kofin Laliga ba, ta bai wa makwafciyarta, Barcelona tazarar maki 9.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu