Isa ga babban shafi

Hukumar Kwallon kafar Ingila ta ci tarar Man City fam dubu dari da 50

Hukumar kwallon kafar Ingila ta ci tarar Manchester City fam dubu dari da 20 bayan da ‘yan wasanta suka yi wa alkalin wasa kawanya a yaayin wasan da suka buga canjaras 3 da 3 da Tottenham a farkon wannan wata na Disamba.

Wasu 'yan wasan Manchester City.
Wasu 'yan wasan Manchester City. Action Images via Reuters - JASON CAIRNDUFF
Talla

‘Yan wasan City da dama ne suka yi wa alkalin wasa Simon Hooper kawanya kusan karshen wasan da suka fafata da Tottenham a ranar 3 ga watan Disamba, bayan da ya dakatar da wasa a yayin da Jack Grealish ya wuce  da kwallo, inda ya yanke hukuncin cewa an rafke Erling Haaland, bayan da tun da farko ya ce a ci gaba da wasa.

Hukumar kwallon kafar ta Ingila ta ce Manchester City ta amsa laifin gazawa wajen tabbatar da ‘yan wasanta sun nuna tarbiya a daidai minti na 94 da fara wasa.

Wasan na City da Tottenham ya zama canjaras ne sakamakon kwallon da Dejan Kulusevski ya saka a daidai minti na 90, bayan da ‘yan Manchester City suka zata sun lashe wasan biyo bayan kwallon da Grealish ya ci a minti na 81.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.