Isa ga babban shafi

Ban damu da sukar da ake kan koma bayan City a Firimiya ba- Guardiola

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Pep Guardiola ya yi ikirarin cewa baya jin komai game da caccakar da ya ke fuskanta dangane da koma bayan da kungiyar ke gani a baya-bayan nan, domin kuwa kungiyar ta gama cimma dukkanin muradan da ta ke fata.

Mai horas da Manchester City Pep Guardiola
Mai horas da Manchester City Pep Guardiola AP - Rui Vieira
Talla

City wadda ta lashe Club World Cup a makon jiya, na ganin koma baya a firimiyar Ingila cikin wannan kaka, kuma a yau ne take shirin karawa da Everton dai dai lokacin da yanzu ta ke matsayin ta 5 a teburin na Firimiya.

Ana dai ganin bayan nasarar City ta lashe kofin zakarun Turai wanda shi ya zama babban kalubale ga Guardiola kungiyar ta sassauto daga yadda aka santa a baya.

A cewar Guardiola yanzu Manchester City ta kammala babi na farko za ta bude wani sabon babin cin nasara a dukkanin wasannin da ke tunkarota.

Bayan doke Fluminense da kwallaye 4 da nema a gasar cin kofin duniya ta kungiyoyi City ta zama kungiyar Ingila 1 tilo da ta taba lashe kofuna har 5 cikin shekara guda.

Manchester City mai rike da kambun gasar zakarun Turai, yanzu haka ta kai matakin wasan rukunin ‘yan 16 inda za ta hadu da Copenhagen a wasanta na gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.