Isa ga babban shafi

Tsohon dan wasan Atlético Diego Costa ya koma Gremio

Diego Costa, mai shekaru 35, ya rattaba hannu a wani sabon kwantragi da Gremio Porto Alegre har zuwa karshen shekara, sanarwar da kungiyar ta Brazil ta fitar a jiya alhamís.Kungiyar ta "cimma yarjejeniya" tare da Diego Costa, wanda zai isa kungiyar a cikin kwanaki masu zuwa don duba lafiyarsa da kuma sanya hannu kan kwantragi har zuwa karshen 2024.

Diego Costa
Diego Costa REUTERS/Eric Gaillard
Talla

 

Kungiyar ta Grêmio na daga cikin kungiyoyin da ke taka rawar a zo a gani a bangaren kwallon kafar Brazil,ta na a mataki na biyu a gasar cin kofin Brazil a 2023, yanzu haka kungiyar na bukatar dan wasan gaba ko mahari tun bayan ficewar tauraruwarta na Uruguay Luis Suarez, wanda ya tafi tare da Lionel Messi a Miami.

Dan wasa Diego Costa
Dan wasa Diego Costa AFP

An haife Diego Costa a Brazil, ya buga wasanni biyu na sada zumunci da kungiyar kwallon kafar Brazil da aka sani da Seleçao, amma kuma ya zama dan kasar Spain,inda a jimilce ya buga wasanni 24,da kuma zura kwallaye 10 da Spain.

 Diego Costa
Diego Costa Atlético de Madrid/AFP/Archivos

Dan wasan ya samu ‘yanci tun karshen kwantraginsa da kungiyar Botafogo, inda ya buga wasa a bara. Tare da Atlético, Costa ya lashe gasar Spain sau biyu (2014, 2021), Europa League sau daya (2018) kuma ya kasance dan wasan karshe a gasar zakarun Turai (2014). Tare da Chelsea, ya lashe gasar Premier sau biyu (2015, 2017).

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.