Isa ga babban shafi

Kotun Faransa ta daure Youcef Atal watanni 8 kan sakon goyon baya ga Gaza

Kotu a Faransa ta yi wa dan wasan gaba na Algeria da ke taka leda da Nice mai doka gasar lig 1 Youcef Atal daurin talala har na tsawon watanni 8 bayan tuhumarsa da wallafa wani bidiyo a shafinsa na sada zumunta da ke da alaka da addini dangane da kisan kiyashin da Isra’ila ke yi wa al’ummar yankin Gaza.

Dan wasan Algeria Youcef Atal da Faransa ta daure watanni 8 saboda sakon nuna goyon baya ga Falasdinawa.
Dan wasan Algeria Youcef Atal da Faransa ta daure watanni 8 saboda sakon nuna goyon baya ga Falasdinawa. AFP - LOIC VENANCE
Talla

Kotun ta bayyana cewa, bidiyon na Atal zai haddasa tsana ta hanyar amfani da addini wanda kuma kai tsaye ke goyon bayan ta’addanci bayan da bidiyon ke addu'ar neman nasara ga al'ummar Gaza.

Kotun hukunta manyan laifuka ta birnin Nice ta kuma ci tarar Atal yuro dubu 45 dangane da bidiyon yayinda a bangare guda kungiyarsa ta dakatar da shi.

Matashin dan wasan mai shekaru 27 wanda ke sahun ‘yan wasan da za su wakilci Algeria a gasar cin kofin Afrika da ke tafe cikin watan nan, tuni ya nemi yafiya kan bidiyon da ya wallafa wanda ya ce tun a lokacin ya goge shi.

Sakon bidiyon na Atal dai na dauke da malamin addini Mahmoud al-Hasanat wanda ke bayani kan kisan kare dangin da Isra’ila ke yi wa Falasdinawa tare da addu’ar Allah ya basu nasara kan Isra’ila.

A cewar kotun, bidiyon na Atal baya kunshe da kalaman neman zaman lafiya face kalaman nuna kyama ga Yahudawa wanda ke matsayin babban zunubi.

Zuwa yanzu Isra’ila ta kashe Falasdinawan da yawansu ya haura dubu 22 daga ranar 7 ga watan Oktoba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.