Isa ga babban shafi

Pape Sarr na Senegal ya tsawaita yarjejeniyar zama a Tottenham zuwa 2030

Dan wasan tsakiya na Tottenham, Pape Matar Sarr ya rattaba hannu a sabuwar yarjejeniyar tsawaita kwantiraginsa da kungiyar wadda za ta bashi damar sake shafe akalla shekaru 6 da rabi.

Pape Matar Sarr na Senegal da ke taka leda da Tottenham.
Pape Matar Sarr na Senegal da ke taka leda da Tottenham. © REUTERS/Daniele Mascolo
Talla

Sarr dan Senegal mai shekaru 21, cikin wannan kaka ya dokawa Tottenham wasanni 18 tare da taimakawa kungiyar kai wa matsayin ta 5 a teburin Firimiya tazarar maki 6 tsakaninta da jagora Liverpool.

Sabuwar yarjejeniyar ta Sarr na nuna cewa zai ci gaba da zama a Tottenham har zuwa nan da kakar wasa ta 2030.

Senegal dai ta sanya sunan matashin dan wasan a cikin tawagar da za ta wakilce ta yayin wasan cin kofin Afrika da ke tafe cikin watan nan, sai dai akwai tantamar yiwuwar zuwansa Ivory Coast musamman bayan raunin da ya samu a wasan da Tottenham ta yi nasara kan Bournemouth da kwallaye 3 da 1.

Tottenham ba ta fitar da cikakken bayani kan ko Sarr zai shafe lokaci mai tsawo yana nyar raunin ko akasin haka ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.