Isa ga babban shafi

Tazarar maki 6 cal ke tsakanin kungiyoyin firimiya 5 da ke tseren lashe kofi

Wata sarkakiya da ke tattare da saman teburin Firimiyar Ingila a bana shi ne kasancewar maki 6 ne cal ke matsayin tazara tsakanin kungiyoyi 5 wadanda dukkaninsu ke fafutukar ganin sun lashe kofin gasar.

Yanzu haka dai Liverpool ke jagorancin teburin na Firimiya.
Yanzu haka dai Liverpool ke jagorancin teburin na Firimiya. REUTERS - MOLLY DARLINGTON
Talla

Tarihi dai na kokarin maimaita kansa game da irin artabun da kungiyoyin na Firimiya suka yi a kakar wasa ta shekarar 1992 da ta 1996, inda a irin wannan lokaci na karshen Disamba aka samu makamanciyar wannan tazara tsakanin kungiyoyin 5 na saman teburin gasar.

Yanayin tseren kungiyoyin 5 na nuna cewa komi ka iya faruwa kuma kowacce a cikinsu ka iya lashe kofin, tseren da sau biyu kadai aka taba ganin irinsa a tarihin gasar kafin sake ganin faruwarsa a bana.

Tun farko Tottenham ta fara samun damar darewa saman teburin karkashin sabon manajanta Ange Postecoglou amma kuma Manchester City ta yo kasa da ita cikin watan Nuwamba, har aka fara tunanin kai tsaye kungiyar wadda ke rike da kambu ce za ta sake lashe kofin, sai dai kuma itama ta rikito bayan rashin nasara a wasanni 5 cikin 6 da ta doka.

Bayan nasarar Arsenal na karbe jagorancin teburin ne kuma Liverpool ta zo daga bisani tare da shiga gabanta, inda masu sharhi suka fara hasashen yiwuwar Arsenal ta koma matsayin bayan karawar ta jiya amma kuma labari ya sha bambam.

Bisa al’ada akan yi hasashen kungiyar da za ta lashe kofin na Firimiya ne a makon karshe na shekara ko kuma zuwa farkon Janairu, sai dai a wannan karon masu sharhi na ganin komi ka iya faruwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.