Isa ga babban shafi

Iyalan Glazer sun rasa karfin fada aji akan Manchester United

Wasu bayanai na nuna cewa Iyalan gidan Glazer wato mamallakan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ka iya biyan Sir Jim Ratcliff kudin da yawansa ya kai miliyan 66 ko fam miliyan 52 matukar suka yi yunkurin soke yarjejeniyar da ke tsakaninsu.

Yanzu haka Sir Jim Ratcliffe shi ke rike da kashi 25 na Manchester United.
Yanzu haka Sir Jim Ratcliffe shi ke rike da kashi 25 na Manchester United. © AFP / OLI SCARFF
Talla

Karkashin yarejeniyar bangarorin biyu da ta bai wa Sir Ratcliff damar jan ragamar kashi 25 na kungiyar, iyalan na Glazer basu da cikakkiyar cewa a kungiyar har sai da sahalewar Ratcliff batun da ake ganin zai yi wuyar dabbakawa.

Yarjejeniyar dai na nuna cewa dole sai da sahalewar Ratcliff Manchester United za ta iya ciniki walau sayarwa ko kuma sayen dan wasa hatta a kakar wasan da ke tafe cikin watan Janairu, kuma aikata duk wani ciniki a boye zai kai su ga biyanshi dala miliyan 66.

Bugu da kari Iyalan na Glazer wadanda a baya su kadai ke da cewa a Manchester United hatta a abin da ya shafi kora ko daukar ma’aikaci a yanzu ba za su iya korar hatta Manaja Erik ten Haq ba sai da sahalewar Ratcliff.

Tuni dai sabon mamallakin kashi 25 na kungiyar wato shi Sir Jim Ratcliff ya gabatar da wani kudiri na shekaru 8  da ke dauke da yadda za a sauya fasalin kungiyar don gogayya da takwarorinta manyan kungiyoyin Turai.  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.