Isa ga babban shafi

Ronaldo ya zama dan wasa mafi zura kwallo cikin shekarar 2023

Dan wasan gaba na Portugal da ke taka leda da Al Nassr ta Saudiya, Cristiano Ronaldo ya zama dan wasa mafi zura kwallaye a shekarar da muke shirin bankwana da ita ta 2023.

Cristiano Ronaldo na Portugal da ke taka leda da Al Nassr ta Saudiya.
Cristiano Ronaldo na Portugal da ke taka leda da Al Nassr ta Saudiya. © AFP - FAYEZ NURELDINE
Talla

Bayan nasarar Al Nassr kan Al Ittihad a Talatar da ta gabata, a jumlace Ronaldo mai shekaru 38 ya zura kwallaye 53 a wasanni 58 tare da taimakawa a zura wasu 15, yayinda ya ke da sauran wasanni gabanin karshen shekara.

Wannan adadi na kwallayen Ronaldo na nufin cewa dan wasan wanda ke gab da cika shekaru 39 a watan Fabarairu mai zuwa, ya dara dukkanin takwarorinsa na Turai da Amurka da kuma Asiya a yawan kwallaye cikin wannan shekara, har kuwa da ‘yan wasan da ake ganin suna kan ganiyarsu.

Dan wasan da ke bin vayan Ronaldo shi ne Harry Kane na Ingila da ke taka leda da Bayern Munich ta Jamus wanda ya zura kwallaye 53 a wasanni 57 yayinda Kylian Mbappe ke matsayin na 3 da kwallaye 52 shima a wasanni 57.

Dukkanin ‘yan wasan biyu babu yiwuwar su iya kara yawan kwallayen na su lura da yadda suka kawo karshen wasanninsu na 2023.

Dan wasan guda da aka yi hasashen ya iya zarta Ronaldo a yawan kwallaye shi ne Erling Haaland, said ai gabaki daya ya iya zura kwallaye 60 ne a wasanni 60 da ya dokawa Manchester City, yayinda rauni ya hana shi haskawa a wasannin cin kofin duniya na kungiyoyi haka zalika babu tabbas kan yiwuwar ya haska a wasan ranar Asabar tsakaninsu da Sheffield United.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.