Ronaldo ya kafa tarihin yawan kwallaye a 2023 a duniya
Cristiano Ronaldo ya kammala shekarar 2023 a matsayin dan wasan da ya fi zura kwallaye a raga a duniya.
Wallafawa ranar:
Dan wasan ya jefa kwallonsa ta 54 kuma ta karshe a shekarar da muka yi ban-kwana da ita a fafatawar da kungiyarsa ta Al Nassr ta lallasa Al-Taawoun da ci 4-1 a gasar lig ta Saudiya.
Ronaldo ya jefa kwallaye 44 a wasanni 50 tun daga watan Janairu, lokacin da ya fara taka leda a Al Nassr ta Saudiya.
Sannan ya jefa kwalllaye 10 a wasannin kasa da kasa da ya buga wa Portugal a 2023, abin da ke nuni da cewa, yana da kwallaye 54 cikin wasanni 59 da ya buga a jumulce a bara.
Sauran ‘yan wasa da suka zura kwallayen da suka kai 50 a sassan duniya a bara, sun hada da Harry Kane da Kylian Mbappe da dukkaninsu ke da kwallaye 52, sai kuma Erling Haaland mai kwallaye 50.
Ronaldo wanda ya saba kafa tarihi a duniyar tamola, a cikin watan Yunin bara ne ya zama dan wasa na farko bangaren maza da ya buga wasannin kasa da kasa har 200, yayin da ya kasance wanda ya fi yawan kwallaye a wasannin kasa da kasa, inda yake da kwallaye 128.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu