Isa ga babban shafi

Ibtila'in 1989: Iyalan magoya bayan Liverpool za su samu tallafin Ingila

Gwamnatin Birtaniya ta gabatar da wata sabuwar doka da zata rika biyan diyya ga mutanen da ibtila’in Hillsborough ya rutsa da su a 1989, tare da neman afuwar ‘yan kasar sakamakon tsaikon da aka samu.

Shekaru 34 kenan da faruwar wannan ibtila'i mafi muni a tarihin kwallon kafar kasar Ingila.
Shekaru 34 kenan da faruwar wannan ibtila'i mafi muni a tarihin kwallon kafar kasar Ingila. © AP
Talla

Wannan na zuwa ne, bayan sama da shekaru shida da gabatar mata da wani rahoto kan halin da iyalan wadanda al’amarin ya rutsa da su.

Wannan ibtila’I na Hillsborough da ya auku a wancan lokaci, ya yi sanadin mutuwar magoya bayan Liverpool 97, a lokacin wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin FA.

Mutuwar magoya bayan kungiyar Liverpoool ta faru ne, sakamakon ruftawar filin wasa na Hillsborough a Sheffield, yayin wasan kungiyar da Nottingham Forest a ranar15 ga Afrilun 1989.

Wannan dai shine ibtila’I mafi muni a tarihin kwallon kafar kasar Ingila.

Masu fafutuka dai tun a wancan lokacin, na neman a samar da wata doka ta musamman da zata rika biyan diyya ga iyalan wadanda abin ya rutsa da su, da kuma gudanar da cikakken bincike kan musabbabin faruwar lamarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.