Isa ga babban shafi

Di Maria ya sanar da yin ritaya daga duniyar tamola

Dan wasan gaba Argentina, Angel Di Maria ya sanar da aniyarsa na rataye takalmansa daga duniyar tamola, amma da zarar an kamala gasar Copa America na kasashen Kudancin Amurka.

Angel Di Maria kenan lokacin da yake murnar kwallon da ya ciwa kasarsa ta Argentina a gasar cin kofin duniya.
Angel Di Maria kenan lokacin da yake murnar kwallon da ya ciwa kasarsa ta Argentina a gasar cin kofin duniya. AP - Natacha Pisarenko
Talla

Dan wasan mai shekaru 35 zai yi ritaya daga kwallon kafa, bayan ya kwashe tsawon shekaru 15 yana wakiltar kasarsa.

Di Maria ya bugawa Argentina wasanni 136 tun daga lokacin da ya fara taka mata leda a shekarar 2008, inda ya fafata a gasar cin kofin duniya har sau hudu, haka zalika ya ciwa kasar kwallo a wasan karshe da suka fafata na gasar cin kofin duniya da Faransa a shekarar 2022.

Zai halarci gasar Copa America karo na shida kenan a tarihinsa, kuma na karshe, a ranar 20 ga watan Yuli, wadda za ta gudana a Amurka, inda ake as ran Argentina za ta kare kambunta ko kuma kasin haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.