Isa ga babban shafi

Arsenal tace ta gaji da karbar tayin afuwa daga alkalan wasa

Duniya – Kungiyar Arsenal dake Ingila ta bayyana goyan bayan ta a kan cacakar da manajan ta Mikel Arteta ya yiwa alkalancin karawar da suka yi da Newcastle wanda ya bayyana shi a matsayin abin kunya.

'Yan wasan kungiyar Newcastle
'Yan wasan kungiyar Newcastle © Scott Heppell/AP
Talla

Arteta cikin fushi ya bayyana bacin ransa da yadda na’urar tantance aikata laifi ta VAR ta kasa gano irin kura kuran da aka samu guda 3 abinda ya baiwa alkalin wasa damar amincewa da kwallon da Anthony Gordon ya jefa wanda ya kawo karshen tafiyar da kungiyarsa ke yi a firimiya ba tare da shan kashi ba.

Daga cikin zarge zarge guda 3 da Arteta ya yi magana a kai, akwai ficewar kwallo daga fili da ture mai tsaron baya Gabriel Magalhaes da Joelinton yayi, da kuma satar fagen da Gordon ya yi.

Kocin Arsenal Mikel Arteta
Kocin Arsenal Mikel Arteta REUTERS/Eddie Keogh

Arteta yace bai dace a ce sakamakon wasan ya tsaya ba, saboda abin kunyar da ya faru, ganin yadda ake kururuta gasar firimiya a matsayin mafi inganci a duniya.

Manajan Arsenal yace ya kwashe shekaru 20 a Ingila, amma a halin yanzu yana jin kunyar abinda ya faru.

Kungiyar Arsenal bayan goyan bayan da ta baiwa Arteta, ta kuma bukaci a daga darajar alkalancin wasan ya kai mizanin irin ci gaban da ‘yan wasan da ake da su ke da shi da kuma kwarewar masu horar da kungiyoyin wasannin.

A kakar wasan da ya gabata, shugaban alkalan wasannin firimiya ya nemi gafarar Arsenal a kan yadda aka amince da kwallon da Brentford ta ci kungiyar, suka kuma tashi 1-1 saboda yadda aka ki amfani da na’urar VAR.

Ita ma kungiyar Liverpool ta bayyana cewar kimar alkalancin wasan na zubewa saboda yadda aka hana su kwallon da suka farke lokacin karawar su da kungiyar Tottenham a watan Satumba.

Mai horar da Liverpool Jurgen Kloop ya bukaci sake buga wasan, amma shugabannin dake kula da gasar suka ki.

Kungiyar Arsenal tace ta gaji da kabar neman afuwa daga hukumar gasar firimiya, inda ta bukaci hukumar dake kula da gasar da ta gaggauta daukar mataki a kan yadda kimar alkalancin wasan ke zubewa.

Arsenal tace tana goyan bayan matakan da shugaban alkalan wasan Howard Webb ke dauka, kuma a shirye take ta yi aiki tare da shi domin daga darajar alkalancin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.