Isa ga babban shafi

Tsohon dan wasan tawagar Ingila da United Sir Bobby Charlton ya rasu

Tsohon dan wasan tawagar Ingila da suka samu nasarar lashe gasar kofin duniya a shekarar 1966 Sir Bobby Charlton, ya rasu ya na da shekaru 86.

Tsohon dan wasan Ingila Bobby Charlton, wanda ke cikin tawagar kasar da suka samu nasarar lashe kofin duniya a shekarar 1966.
Tsohon dan wasan Ingila Bobby Charlton, wanda ke cikin tawagar kasar da suka samu nasarar lashe kofin duniya a shekarar 1966. AFP
Talla

A cikin sakon mutuwarsa da iyalansa suka fitar, sun ce da sanyin safiyar Asabar din nan ce tsohon dan wasan gaban ya rasu.

Charlton ya samu nasarar bugawa kasarsa wasanni 106 tare da jefa kwallaye 49, lamarin da ya bashi damar kafa tarihin yawan zura kwallo a karninsu.

A zaman shekaru 17 da yayi a kungiyar Manchester United, Charlton ya bugawa kungiyar wasanni dari 758, inda yayi nasarar lashe gasar lik din Ingila 3 da kofin kalubale da kuma kofin zakarun Turai a shekarar 1968, harma ya jefa kwallaye biyu a wasan karshe da suka yi da Benfica.

Tsohon dan wasan Manchester United Sir Bobby Charlton.
Tsohon dan wasan Manchester United Sir Bobby Charlton. AFP - TED ALJIBE

Tuni dai kungiyar Manchester United ta mika sakon ta’aziya ga iyalan mamacin tare kuma da karramashi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.