Isa ga babban shafi

Dole 'yan wasan Ingila su jajirce - Southgate

Kocin Ingila, Gareth Southgate ya ce jagorancin babbar tawagar kwallon kafar Ingila wani babban kalubale ne a wannan lokaci mai cike da sarkakiya, kuma ya ce akwai bukatar jajircewa a tattare da ‘yan wasan tawagar.

Kocin babbar tawagar kwallon kafar Ingila, Gareth Southgate.
Kocin babbar tawagar kwallon kafar Ingila, Gareth Southgate. AFP/File
Talla

Ingila sun samu koma baya zuwa rukunin ‘yan dagaji a gasar kasashen Turai ta Nations League, bayan da Italiya suka lallasa su da ci 1 mai ban haushi ranar Juma’a a birnin Milan.

Za su fafata da Jamus a ranar Litinin din nan, bayan da suka buga wasanni har 5 ba tare da nasara ba a karon farko tun shekarar 2014.

Southgate ya ce haka lamarin yake wani lokaci, kuma ba shi ne koci na farko da ya taba jagoranatar tawagar a lokaci mai cike da jarawaba irin wannan ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.