Isa ga babban shafi

Ana zargin kocin tawagar mata na Zambia da lalata

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA na gudanar da bincike kan manajan tawagar kwallon kafar ‘yan matan Zambia Bruce Mwape kan wani sabon zargin aikata lalata.

Tawagar 'yan wasan mata na Zambia bayan doke Costa Rica a gasar cin kofin duniya.31/07/23
Tawagar 'yan wasan mata na Zambia bayan doke Costa Rica a gasar cin kofin duniya.31/07/23 REUTERS - DAVID ROWLAND
Talla

An fitar da tawagar Zambia daga gasar cin kofin duniya a matakin rukuni, bayan da ta sha kashi har sau biyu a hannun Japan da Spain, duk da cewa sun kammala gasar na nasara a wasan da suka doke Costa Rika da ci 3-1 a ranar Litinin da ta wuce.

Sai dai a cewar jaridar The Guardian, ana zargin Mwape da shafa kirjin daya daga cikin 'yan wasansa mata kwanaki biyu kafin wasansu na karshe.

Jaridar wasanni ta Mail Sport ta ruwaito cewa tun cikin watan da ya gabata, Mwape, wanda ke jan ragamar kungiyar kwallon kafar matan na Zambia tun a shekarar 2018, FIFA na bincike kan wasu zarge-zargen da ake masa na lalata da mata– ko da yake kocin ya musanta duk wadannan zarge-zarge.

Rahoton ya ce FIFA ta tabbatar da cewa ta samu korafi a hukumance bayan da ‘yan wasa da dama suka shaida yadda Mwape ke aikata abin da bai dace ba, kamar yadda wata majiya ta shaida. “Bai dace koci ya taba mamar ‘yan  wasa ba”.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.