Isa ga babban shafi

City ta yi kankankan da United wajen kafa tarihin lashe kofuna 3 a kaka guda

Bayan nasarar kungiyar kwallon kafa ta Manchester City wajen lashe kofin zakarun Turai inda ta doke Inter Milan da kwallo 1 mai ban haushi, kungiyar ta goge guda cikin tarihin da takwararta Manchester United ke tunkaho da shi wato lashe kofunan mabanbantan gasa har guda 3 a kaka guda.

Tawagar kwallon kafa ta Manchester City bayan lashe kofin zakarun Turai.
Tawagar kwallon kafa ta Manchester City bayan lashe kofin zakarun Turai. REUTERS - MOLLY DARLINGTON
Talla

Guardiola ya lashe kofin FA bayan doke Manchester United kana ya yi kasa da Arsenal wajen lashe firimiyar Ingila daga bisani kuma ya je Istanbul ya doke Inter Milan a wasan karshen na zakarun Turai, nasarar lashe wadannan kofuna 3 ta bashi damar yin kankankan da zakakurin Manajan Manchester United wato Sir Alex Ferguson wanda ke matsayin manaja daya tilo a Ingila da ya taba hada wannan kofuna a kakar wasa ta 1998 zuwa 1999.

Yanzu haka dai kungiyoyin nan biyu na birnin Manchester wato City da United su kadai ke da tarihin lashe kofunan 3 a kaka guda, ko da ya ke a kaf nahiyar Turai akwai kungiyoyi irinsu Celtic da Ajax wadanda su ne na farko da suka kafa wannan tarihi Celtic a kakar wasa ta 1966 zuwa 1967 sai Ajax a kakar wasa ta 1971 zuwa 1972.

Sauran kungiyoyin da suka taba nasarar lashe kofunan 3 a Turai sun kunshi PSV Eindhoven da Manchester United kana Barcelona sai Inter Milan da kuma Bayern Munich ta Jamus.

Masu sharhi kan harkokin wasannin suka ce Manchester City ba ta iya samun damar kai wa ga wannan nasara ta lashe kofin zakarun Turai karon farko a tarihi ba, bayan yunkurin lashe kofin sau 13 ciki har da kai wa wasan karshe amma Chelsea ta maketa sai da ta karya dokoki 115 wanda yanzu haka ta ke fuskantar tuhuma akai.

Nasarar dai ta zamo babban dako da Manchester City ta shafe tsawon lokaci ta na yi tun bayan saka kafarta karon farko a gasar cikin kakar wasa ta 1969, kuma daga kakar wasa ta 2012 zuwa yanzu anga yadda kungiyar ta kai wasannin gab da na kusa da karshe sau 3 sai wasan gab da karshe sau 2 kana wasan karshe shima sau biyu gabanin samun nasarar.

Mutane da dama na kallon zuwan Haaland Manchester City a matsayin wata gagarumar gudunmawa da ta kai kungiyar ga nasarar lashe wannan kofi na gasar zakarun Turai da ta shafe tsawon lokaci ta na nema da kuma zuba makuden kudade, masu sharhi kan wasanni na Turai na ganin gudunmawar ta Haaland ba wata abar azo a gani ba ce idan an kwatanta da sadaukarwar wasu tarin ‘yan wasa a tafiyar ciki kuwa har da Kevin de Bruyne da Ilkay Gundogan baya ga Jack Grealish dama Bernado Silva.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.