Isa ga babban shafi

City ta kai wasan garshe na zakarun Turai bayan doke Madrid da kwallaye 4 da nema

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta lallasa Real Madrid mai rike da kambun gasar zakarun Turai a wasan gab da na karshe, nasarar da ta bai wa jagorar Firimiyar damar kai wa wasan karshe na gasar inda za ta hadu da Inter Milan a Istanbul.

Tawagar Manchester City.
Tawagar Manchester City. AFP - OLI SCARFF
Talla

An dai ta shi wasan na jiya kwallaye 4 da nema wanda ke nuna huce haushin City kan tawagar ta Carlo Ancelotti da ta fitar da ita daga gasar sau 2 a irin wannan mataki, kuma a jumulla Manchester City ta yi nasara da kwallaye 5 da 1 idan hada da haduwar ta da Real Madrid a wasan farko.

Yayin wasan na jiya dai Bernado Silva ne ya zama dan wasa mafi hazaka bayan kwallayensa biyu a minti na 23 da kuma minti na 37 da suka baiwa City gagarumin rinjaye tun a zagayen farko na wasan.

Duk da cewa Coutois ya yi nasarar tare kwallaye 2 da Haaland ya nufaci zurawa tun a zagaye na farko amma wannan rashin nasarar ta jiya ta zama wasa mafi muni da Madrid ta yi a baya-bayan nan karkashin gasar ta cin kofin zakarun Turai.

Kamar dai yadda wasan farko ya gudana kowanne bangare ya kange ‘yan wasan gaba na abokiyar karawarsa da ake fargabar su iya zura kwallo, ta yadda aka gaza ganin tasirin ‘yan wasan irinsa Haaland da De Bruyne ko da ya ke ya taimaka wajen zura kwallaye 2 haka zalika Karim Benzema da Vinicius Junior har ma da Rodrygo da suka gaza katabus.

Manchester City wadda ke shirin dage kofin Firimiya da zarar ta yi nasara a haduwarta da Chelsea ranar lahadin nan ta na kuma tunkarar wasan karshe na cin kofin FA da za ta hadu da Manchester United a wasan karshe, wannan na nuna cewa ta na tunkarar kofuna 3 a cikin wannan kaka.

A ranar 10 ga watan Yuni ne dai za a doka wasan karshe tsakanin Cityn wadda ba ta taba lashe kofin gasar ba da kuma Inter Milan da ta lashe kofin sau 3 wato a shekarun 1964 da 1965 da kuma 2010 wanda ya zama lokaci na karshe da ta kai matakin wasan karshe, wato shekaru 13 da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.