Isa ga babban shafi

Da yiwuwar rauni ya hana Camavinga shiga wasan Real Madrid da Manchester City

Da yiwuwar Real Madrid ta yi tattaki zuwa Etihad gobe laraba ba tare da dan wasanta Eduardo Camavinga ba, bayan raunin da ya samu a wasan da Madrid ta yi nasara kan Getafe a karshen mako.

Eduardo Camavinga na ci gaba da haskawa a Real Madrid tun bayan sayensa daga Rennes ta Faransa.
Eduardo Camavinga na ci gaba da haskawa a Real Madrid tun bayan sayensa daga Rennes ta Faransa. REUTERS - SUSANA VERA
Talla

Raunin na Camavinga dai babban kalubale ne ga tawagar Carlo Ancelotti da ke fatan kai wa wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Turai idan har ta iya nasara a haduwar ta gobe tsakaninta da Manchester City, wadda a haduwar farko suka tashi wasa kunnen doki wato daya da daya.

Camavinga dai ya taka muhimmiyar rawa a canjaras din Madrid da City makon jiya, haka zalika anga rawar da ya taka a nasarar bara da Madrid din ta fitar da City daga gasar dalilin da ya sa ake kallon tasirinsa a cikin tawagar ta Ancelotti yayin wasan na gobe.

Duk da cewa ana ganin Camavinga a sahun wadanda suka tafka kuskuren da ya bai wa Kevin De Bryune damar farko kwallon da Vinicius ya zura a makon jiya amma lura gurbin da ya ke rikewa a cikin tawagar Ancelotti ka iya haduwa da matsala a wasan na gobe.

Madrid wadda ke rike da kambun gasar na zakarun Turai na neman yin dukkan mai yiwuwa don kare kambunta yayinda Manchester City ke ci gaba da kishirwar kofin wanda har zuwa yanzu ta gaza kai wa gida duk kuwa da tsabar kudin da ta zuba wajen sayen manyan 'yan wasa da kuma kawo shi Pep Guardiola.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.