Isa ga babban shafi

Wasan Manchester City da Real Madrid zai ja hankalin magoya baya

Yau ake shirin barje gumi tsakanin Real Madrid da Manchester City a wasan gab da na karshe na gasar cin kofin zakarun Turai, wasan da aka jima ana dakonsa don ganin yadda za ta kaya tsakanin manyan kungiyoyin biyu.

Tawagar Real Madrid yayin atisayen tunkarar Manchester City a wasan gab da na karshe na cin kofin zakarun Turai.
Tawagar Real Madrid yayin atisayen tunkarar Manchester City a wasan gab da na karshe na cin kofin zakarun Turai. AP - Paul White
Talla

Duk da cewa Real Madrid na da tarihin lallasa Manchester City, amma kuma a yanzu wasu na ganin Cityn ta kara karfi musamman bayan zuwan Erling Haaland daga Borussia Dortmund da ya kange kungiyar daga shan kaye.

Tuni dai masu sharhi kan al’amuran wasanni suka fara tsokaci kan wannan haduwa ta yau wadda za a yi a gidan Madrid, inda Michael Brown tsohon dan wasan Manchester city ke ganin dole ne ‘yan wasan na Guardiola su kaucewa kuskure a haduwar ta yau don kaucewa abin da ya faru a bara.

Ko a baran ma dai Real Madrid ce ta yi waje da City a irin wannan mataki bayan nasara da kwallaye 6 da 5 a jumullar haduwa biyun da suka yi.

Ana ganin dai Pep Guardiola zai iya amfani da salon zubin ‘yan wasan da ya yi a haduwarsu da Arsenal don kaucewa fuskantar matsala kwatankwacin wadda ya hadu da ita a haduwarsu ta bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.