Isa ga babban shafi

Real Madrid ta sake fitar da Chelsea daga gasar zakarun Turai

Real Madrid ta sake lallasa Chelsea har gida da 2-0 yayin fafatwar da suka yi karo na biyu a zagayen kwata final na gasar Zakarun Turai.

'Yan wasan Real Madrid yayin murnar jefawa Chelsea kwallon farko a karawar  da suka yi a daren  ranar Talata, 18 ga Afrilun 2023.
'Yan wasan Real Madrid yayin murnar jefawa Chelsea kwallon farko a karawar da suka yi a daren ranar Talata, 18 ga Afrilun 2023. AP - Kirsty Wigglesworth
Talla

A wasan farko ma dai Madrid din ce ta doke kungiyar ta Chelsea da 2-0 a Spain, abinda ya sanya jimillar kwallayen da aka jefa mata a raga kai wa 4-0 a wasanni biyun da suka fafata.

Dan wasan gaba na Real Madrid Rodrygo Goes ne ya jefa dukkanin kwallayen a ragar Chelsea a mintuna na 58, sai kuma ta biyu, a yayin da ya rage mintuna 10 a karkare wasan.

A halin yanzu akwai yiwuwar Real Madrid za ta sake haduwa da Manchester City a zagayen wasan kusa da na karshen gasar zakarun Turai, la’akari da cewar City ke kan gaba a wasan da za ta buga da Bayern Munich a yau Laraba, bayan da ta lallasa ta da kwallaye 3-0 yayin haduwarsu ta farko a makon jiya.

A bangaren Chelsea lamurra ba su yi wa kungiyar daidai ba, duk da cewar sabon shugabanta Toed Bhoely ya kashe fiye da fam miliyan 500 wajen cefanen sabbin ‘yan wasan da yayi fatan za su dawo da martabar Kulob din.

Sai dai bayan ficewa daga gasar zakarun Turai, kungiyar ta Chelsea a yanzu tana matsayi na 11 a gasar Premier Ingila, wanda kuma abu ne mawuyaci ta iya samun tikitin halartar gasar cin kofin zakarun Turai mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.