Real Madrid ta casa Liverpool da kwallaye 5 da 2 har gida a gasar zakarun Turai
Liverpool ta baras da damar daukar fansar rasa wasan karshen gasar zakarun Turai ta bara kan Real Madrid yayin karawar da suka yi a daren jiya, inda zakarun na Spain suka yi tattaki har gida filin wasa na Anfield suka lallasa kungiyar ta Liverpool da kwallaye 5-2.
Wallafawa ranar:
Da fari dai kamar nasara na hannun masu masaukin bakin, domin a cikin mintuna 14 ‘yan wasan Liverpool Darwin Nunez da Muhd Salah suka jefa kwallo guda guda a ragar ‘yan Madara.
Sai dai daga bisani ‘yan wasan Real Madrid Vinicius Junior ya rama kwallayen biyu, Eder Militao ya kara ta uku, yayin da Karim Benzema kuma ya ci Karin kwallaye 2.
A halin yanzu sai kuma a cikin watan Maris kungiyoyin biyu za su sake karawa a Spain domin tantance wanda zai tsallaka zuwa zagayen wasan Kwata Final.
Tarihi dai ya nuna ya zuwa yanzu a haduwar da suka yi sau 10 Real Madrid ta samun nasara a wasanni 6, sun yi canjaras sau 1, yayin da Liverpool ta samu nasara sau 3.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu