Isa ga babban shafi

Faransa ta amsa laifin azabtar da masu kallon wasan Real Madrid da Liverpool

Ministan cikin gidan Faransa Gerald Darmanin ya nemi gafara akan yadda 'yan sandan kasar suka yi amfani da hayaki mai sa hawayen da ya wuce kima lokacin wasan karshe na cin kofin zakarun nahiyar Turai tsakanin kungiyar Real Madrid da Liverpool a karshen mako.

Tawagar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid bayan nasarar lashe kofin zakarun Turai.
Tawagar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid bayan nasarar lashe kofin zakarun Turai. © AFP - PAUL ELLIS
Talla

Yayinda ya gurfana a gaban Majalisar Dattawa domin amsa tambayoyi akan korafe korafen da suka biyo bayan wasan karshe na cin kofin zakarun nahiyar Turan, ministan ya ce amfani da hayaki mai sa hawayen ya hana samun tirmitsitsi wajen shiga filin wasan, sai dai ya ce abin takaici hayakin ya yiwa kananan yara illa.

Saboda haka ministan wanda ya bayyana cewar akalla mutane sama da 110, 000 suka ziyarci filin wasan karshen, ya nemi gafara game da amfani da hayakin mai sa hawaye, yayin da ya ce za a hukunta jami’an 'yan Sandan da suka harba hayakin.

Shugaba Emmanuel Macron ya bukaci gudanar da bincike na hakika dangane da lamarin, lura da yadda ministan cikin gidan ke ci gaba da fuskantar tuhuma dangane da rawar da 'yan Sanda suka taka.

Ministan ya ce akalla magoya bayan Liverpool 30,000 zuwa 40,000 suka je filin ba tare da tikitin shiga wasan ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.