Isa ga babban shafi

Benzema na Real Madrid ya zama gwarzon gasar zakarun Turai a bana

Dan wasan gaba na Real Madrid Karim Benzema ya zama gwarzon gasar zakarun Turai na bana bayan zura kwallaye 15 da kuma kai kofin gida bayan nasarar tawagarsa a wasan karshe na gasar.

Karim Benzema dan wasan gaba na Real Madrid.
Karim Benzema dan wasan gaba na Real Madrid. REUTERS - JUAN MEDINA
Talla

Benzema dan Faransa mai shekaru 34 da ke dage kofin karo na 5 a tsawon lokacin da ya shafe yana take leda da Madrid, wannan nasara ta share masa hanyar yiwuwar iya lashe kyautar Ballon d’Or, amma kinsan da yak e wannan karon akwai gasar cin kofin duniya za a iya cewa sai an jira anga irin rawar da kasarsa za ta take a Qatar kasancewarta mai rike da kambun gasar.

Baya ga Benzema, Vinicius Junior da ya zura kwallo guda tal da ta baiwa Madrid nasara a wasan na asabar din da ta gabata, ya zama matashin dan wasa mafi nuna bajinta a gasar ta bana.

Sauran wadanda suka samu girmama daga UEFA cikin tawagar kaka sun kunshi, dan wasan tsakiyar Real Madrid Luka Modric da mai tsaron raga Thibaiut Courtois.

Sauran sun hada da ‘yan wasa hudud aga Liverpool ciki har da Trent Alexandre-Arnold kana Virgil van Dijk sai Andy Robertson tukuna Fabinho.

Sauran ‘yan wasan da suka shiga tawagar shekarar akwai Kylian Mbappe na PSG da Kevin de Bruyne na Manchester City kana mai tsaron baya na Chelsea Antonio Rudiger.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.