Isa ga babban shafi

Real Madrid ta lallasa Chelsea a gasar zakarun Turai

Kwallayen ‘yan wasan gaba na Real Madrid Karim Benzema da Marco Asensio sun bai wa kungiyar nasara kan Chelsea da 2-0 a wasan farko na fafatawar da suka yi a zagayen wasan kwata final na gasar zakarun Turai.

Dan wasan gaba na Real Madrid Karim Benzema yayin murnar jefa kwallo a ragar Chelsea yayin karawarsu ta zagayen kwata final a gasar zakarun Turai.
Dan wasan gaba na Real Madrid Karim Benzema yayin murnar jefa kwallo a ragar Chelsea yayin karawarsu ta zagayen kwata final a gasar zakarun Turai. REUTERS - JUAN MEDINA
Talla

Benzema ya jefa kwallon farko ne a mintuna na 21, yayin da Asensio ya jefa kwallo ta 2 a mintuna na 74.

Chelsea wadda a yanzu haka ke matsayi na 11 a gasar Firimiyar Ingila sakamakon rashin karsashinta, ta karasa wasan na daren ranar Laraba a filin wasan na Santiago Bernabeu ne da ‘yan wasa 10, bayan jan katin da alkalin wasa ya bai wa Ben Chilwell, saboda ketar da ya yi wa dan wasan Madrid Rodrygo a yayin da ya ke gaf da jefa musu karin kwalllo a raga.

Karo na biyu kenan da Chelsea ke shan kaye a wasan da ta buga a karkakshin sabon kocinta na wucin gadi Frank Lampard, wanda ta sake bai wa aikin horas da ‘yan wasanta a makon jiya, bayan korar mai horas da ita Graham Potter.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.