Isa ga babban shafi

Haaland ya ci kwallo ta 45 yayin da Man City ta lallasa Bayern

Erling Haaland ya ci kwallonsa ta 45 a kakar wasa ta bana bayan da Manchester City ta doke Bayern Munich da ci 3-0 a zagayen farko na wasan daf da na kusa da na karshe na gasar cin kofin zakarun Turai ranar Talata, inda ta kama hanyar haye wa wasan kusa da na karshe.

Dan wasan Manchester City Erling Haaland
Dan wasan Manchester City Erling Haaland REUTERS - MOLLY DARLINGTON
Talla

Rodri da Bernardo Silva na cikin wadanda suka taimakawa zakarun na Ingila, dake hubbasa don lashe babbar gasar a karon farko.

Mintuna 27 da fara wasa City ta ci kwallon ta hannun Rodrigo Hernandez, shi kuwa Bernardo Silva ya kara ta biyu bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, sai kuma Erling Haaland ya ci na uku bayan mintuna bakwai.

Wasa na bakwai kenan suka kara tsakaninsu a Champions League, kuma City ta ci hudu, Bayern ta yi nasara a uku.

Inter Milan

Inter Milan ma ta kam hanyar kai wa matakin wasan dab da na karshe a gasar cin kofin zakarun Turai bayan doke Benfica da ci 2 – 0 bayan da Nicolo Barella da Romelu Lukaku suka ci kwallo guda-guda a Lisbon.

Milan ta ci kwallon farko ta hannun Nicolo Barella, bayan da suka koma karawar zagaye na biyu.

Dan wasan aro a AC Milam Romelu Lukaku, 21/02/21
Dan wasan aro a AC Milam Romelu Lukaku, 21/02/21 AP - Antonio Calanni

Romelu Lukaku, wanda ke wasa amtsayin aro daga Chelsea shine ya zura na biyu a raga a bugun fenariti, saura minti takwas a tashi wasa.

Karo na hudu da suka kece raini a tsakaninsu, inda Inter ta ci uku da canjaras daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.