Isa ga babban shafi

Kuskuren De Gea a wasan mu da West Ham ba komi ba ne- ten Hag

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Erik ten Hag ya ce ba komai ba ne kuskuren da mai tsaron ragar sa David De Gea ya yi a karawar su da West Ham United.

Mai tsaron ragar Manchester United David de Gea.
Mai tsaron ragar Manchester United David de Gea. POOL/AFP/Archives
Talla

A cewar ten Hag kuskure wani bangare ne na wasa, duk da dai wannan ne karo na hudu da De Gea ke yin kuskuren da ake zura masa kwallo a raga.

Wannan nasarar dai da aka samu kan United ta sake maida kungiyar baya a kokarin ta na kammala wannan kaka a cikin jerin kungiyoyi 4 da za su doka gasar zakarun Turai a kaka mai zuwa.

A yanzu dai Manchester United na mataki na hudu a teburin Firimiyar Ingila, inda Liverpool ke biye mata a mataki na biyar, da tazarar maki daya tal duk da cewa dai tawagar ta Ten Hag na da wasa guda a hannu.

Idan har United na son cimma mafarkin ta a zuwa gasar zakarunTurai a shekara mai zuwa, dole ne ta lashe dukkanin wasannin ta 4 da suka yi saura a kakar wasan bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.