Isa ga babban shafi

Zakarun Turai: Milan ta kai zagayen kusa da na karshe karon farko tun 2007

AC Milan ta tsallaka zuwa zagayen wasan kusa da na karshen gasar cin kofin zakarun Turai, bayan wasan da aka tashi 1-1 tsakaninta da Napoli.

'Yan wasan kungiyar AC Milan a lokacin da suke murnar samun nasara akan takwarorinsu na Napoli.
'Yan wasan kungiyar AC Milan a lokacin da suke murnar samun nasara akan takwarorinsu na Napoli. AP - Andrew Medichini
Talla

A wasan farko na karawar da suka yi dai, Milan din ce ta samu nasara da 1-0, abinda ya sa idan aka hada sakamakon haduwa biyu da kungiyoyin suka yi, Napoli ta sha kashi da 2-1.

Dan wasan AC Milan Olivier Giroud ne ya jefa kwallon ta su tilo a wasan na ranar Talata jim kadan bayan barar da  damar bugun fanareti da yayi, yayin da Victor Osimhen dan Najeriya, ya ramawa Napoli ana gaf da tashi daga wasan.

Rabon da AC Milan ta kai zagayen wasan kusa da na karshen gasar zakarun Turai, tun shekarar 2007 lokacin da ta lashe kofin gasar karo na bakwai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.