Isa ga babban shafi

Karon farko Napoli ta kai zagayen dab da na kusa da na karshe a Gasar Zakarun Turai

Mai horas da kungiyar kwallon kafar Eintracht Frankfut Oliver Glasner, ya yabawa  kungiyar Napoli bisa irin rawar da ta taka a karawar su, harma ya ce kungiyar ta taka irin matakin da Bayern Munich ta ke, bayan da tawagar ta sa tasha kashi a hannun jagorar gasar Serie A. 

Muryar zura Frankfut kwallo ta 3 da dan wasan Napoli Piotr Zielinski ya yi.
Muryar zura Frankfut kwallo ta 3 da dan wasan Napoli Piotr Zielinski ya yi. REUTERS - CIRO DE LUCA
Talla

Napoli ta samu nasara ne kan Frankfut da ci 5 da nema a wasannin zagaye na biyu na gasar zakarun Turai, inda a karon farko ke nan kungiyar ta samu gurbi a matakin dab da na kusa da na karshe a gasar. 

Bayan nasarar, dan wasan gaban kungiyar Victor Osimhen da ya samu nasarar jefa kwallaye biyu a wasan na daren jiya, ya ce fatan kungiyar shine samun nasarar lashe gasar ta bana. 

A bana kungiyar ta Napoli ta kama hanyar lashe gasar Serie A a karon farko cikin sama da shekaru 30. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.