Isa ga babban shafi

AC Milan ta fitar da Tottenham daga gasar zakarun Turai

AC Milan ta samu nasarar tsallakawa zagayen dab da na kusa da na karshe a gasar zakarun Turai, bayan da kungiyar ta Italiya ta rike Tottenham da ta karasa wasan da ‘yan wasa 10 aka tashi babu ci.

Wasan Tottenham da AC Milan.
Wasan Tottenham da AC Milan. Action Images via Reuters - MATTHEW CHILDS
Talla

Cire Tottenham dai na zuwa ne bayan da aka cire ta daga kofin FA, lamarin da ya kawo karshen fatan ta na lashe kofi a karon farko a cikin shekaru 15 da suka gaba. 

Mai horas da kungiyar Antonio Conte ya dawo bakin sa ne a wasan na daren jiya bayan da aka yi masa aiki a mafitsarar sa, amma sai dai duk da haka tawagar ta sa ta kasa farke kwallo daya tilo da AC Milan ta jefa mata a raga a karawar farko da su yi. 

An samu tsaikon fara wasan da minti 10 sabida rashin isar kungiyoyin filin wasa da wuri sakamakon cunkoson ababen hawa da suka fuskanta. 

Tottenham ta yi rashin nasara a wasanni 4 daga cikin 6 na baya-bayan da ta yi ciki kuwa harda rashin nasarar ta a karawa ta biyu da suka yi da Sheffield United a gasar FA. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.