Isa ga babban shafi

Mahaifin Haaland ya gamu da fushin magoya bayan Real Madrid

Mahaifin dan wasan gaba na Manchester City Erling Haaland wato Alfie Haaland ya bayyana cewa sai da aka raka shi daga mazauninsa zuwa wani kebantaccen wuri yayin wasan Madrid da City sakamakon yadda magoya baya suka fusata da salon murnarsa bayan Kevin de Bruyne ya farke kwallon Vinicius.

Mahaifin dan wasan gaba na Manchester City Erling Haaland wato Alf-Inge Haaland.
Mahaifin dan wasan gaba na Manchester City Erling Haaland wato Alf-Inge Haaland. AP - Jon Super
Talla

Wasu faya-fayan bidiyo sun nuna yadda mahaifin Haaland ya rika musayar kalamai da magoya bayan na Real Madrid yayin wasan na ranar talata wanda aka tashi kwallo 1 da 1 tsakanin manyan kungiyoyin biyu, gabanin a sauya mishi wurin zama.

Bayan tashi dagga wasan Alfie Haaland ya yi wani rubutu a shafinsa na Twitter ya na cewa ‘‘ Wato basa so muyi murnar kwallon KDB ya na nufin Kevin de Bruyne’’

Yayin da ya kara wani rubutun na daban da ke cewa, za mu matsa gaba tunda ‘yan Madrid basu yi farin ciki da kunnen doki ba.

A minti na 67 ne De Bruyne ya farke kwallon da ya Vinicius ya ci wa Real Madrid dalilin da ya sanya aka tashi wasa kwallo 1 da 1.

Bayan zura kwallon ta Vinicius dai anga yadda mahaifin Haaland ya Mike ya na daga hannayensa duka biyu ga magoya bayan Real Madrid da ke bayansa, yayinda wasu bayanai suka ce har ya jefesu da abincin da ya ke ci ko da ya ke ya musanta batun.

A ranar 17 ga watan nan ne za a yi haduwa ta biyu tsakanin Madrid da City a Etihad Wanda kuma baza izo da sauki ba, lura da yadda aka tashi wasan farko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.