Isa ga babban shafi

Man City da Inter sun shirya haduwa gobe a wasan karshe na gasar zakarun Turai

Gobe Asabar ake shirin doka wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Turai tsakanin Inter Milan da Manchester City, kungiyar da ke neman kafa tarihin lashe babbar gasar ta Turai a karon farko. 

'Yan wasan Manchester City.
'Yan wasan Manchester City. © AP - Tim Goode
Talla

Tun a shekarar 2008 ne lokacin da kungiyar ta koma hannun Larabawan Abu Dhabi, yau shekaru 15 kenan kungiyar Manchester City ta fara fafutukar ganin ta cimma nasarar lashe kofin gasar Zakarun na Turai. 

Masu fashin baki da dama sun fi kyautata zaton cewa City ce za ta samu nasara a wasan na gobe da za ta fafata ta Inter Milan. 

Daga cikin dalilin masu sharhin kuwa akwai ganin yadda kungiyar ba ta yi rashin nasara ko da sau guda ba a gasar zakarun Turai ta bana, yayin da kuma bayan shiga zagayen ‘yan sha shida, da kwata final da kuma semis, kungiyar ta zazzaga wa abokan hamayyar da ta kara da su wato RB Leipzig, da Bayern Munich da kuma Real Madrid kwallaye a raga.  

A bangaren Inter Milan kuwa, sal uku kungiyar ta taba lashe kofin gasar zakarun Turai, sai dai rabon ta da kofin, tun shekarar 2010, lokacin da kulob din ke karkashin Jose Mourinho. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.