Isa ga babban shafi

Gasar zakarun Turai: Burin City ya cika

A karon farko kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta samu nasarar lashe gasar zakarun nahiyar Turai, bayan da ta doke Inter Milan da ci daya mai ban haushi.

'Yan wasan Manchester City ke nan, a lokacin da suka lashe kofin zakarun Turaii.
'Yan wasan Manchester City ke nan, a lokacin da suka lashe kofin zakarun Turaii. AFP - FRANCK FIFE
Talla

Rodri ne ya ci musu kwallo daya tilo a wasan a minti na 68, wanda hakan ya cika fatan su na lashe kofin.

City ta taka rawar gani a wannan kaka wajen lashe manyan kofuna uku, da suka da Firimiyar Ingila da kofun kalubale FA sai kuma na zakarun Turai.

‘Yan wasan na Pep Guardiola a yanzu sun taddo tarihin da Manchester United ta taba kafawa a shekarar 1999 na lashe dukkanin manyan kofuna 3 da suka fafata akai.

City ta dade tana fatan samun nasarar lashe gasar, inda a shekarar 2021 ta kai wasan karshe amma sai dai hakar ta bata cimma ruwa ba domin kashi ta sha a hannun Chelsea a wasan karshe.

A shekarar data gabata ma dai, Manchester City ta yi yunkunrin kaiwa wasan karshe inda Madrid ta taka mata birki a matakin kusa da na karshe.

Sai dai bayan sake inganta tawagar ta hanyar kawo Earling Haaland, City ta cika burin ta.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.