Isa ga babban shafi

Hasashen yadda zata kaya a wasan karshe na gasar zakarun Turai

Nan da sa’oi kadan, za’a fara buga wasan karshe na gasar zakarun Turai tsakanin kungiyar Manchester City da kuma Inter Milan a birnin Istanbul na Turkiya.

Filin da kungiyoyin Inter Milan da Manchester City zasu buga wasan karshe a birnin Istanbul na Turkiya.
Filin da kungiyoyin Inter Milan da Manchester City zasu buga wasan karshe a birnin Istanbul na Turkiya. REUTERS - UMIT BEKTAS
Talla

Manchester City na fatan lashe kofin a karon farko a tarinhin ta, duk da cewa wannan ne karo na biyu da ta taba zuwa wasan karshe a gasar.

Da dama daga cikin masu sharhi kan wannan wasa na ganin City ce za ta samu nasara, lura da cewa bata yi rashin nasara ko sau daya a gasar ta bana ba, domin a  cikin wasanni 12 da ta buga tayi nasarar lashe 7 da kuma kunnen doki a 5, sannan ta zura kwallaye 31 ita kuma aka zura mata biyar kadai.

A bangaren mai horas da kungiyar ta City Pep Guardiola kuwa, yana neman lashe kofin ne a karon farko cikin sama da shekaru 10, tun bayan nasarar lashe shi da yayi a kungiyar Barcelona.  

Guardiola da kungiyoyi da kuma masu horaswa na Italiya

A wasan karshe na shekarar 1994,Guardiola na cikin tawagar Barcelona da suka buga wasan karshe a gasar zakarun Turai da AC Milan, inda ake ganin sun fi AC Milan damar lashe wasan, sai dai reshe ya juye da mujiya inda AC Milan ta lallasu da ci 4 da nema.

Haka nan a wasan kusa da na karshe da Guardiola ya yi da Inter Milan a kakar shekarar 2010 lokacin yana Barcelona, Milan ce ta fidda shi daga gasar kuma ta je ta lashe kofin.

Inter Milan

Inter Milan ba kwanwar lasa ba ce a gasar zakarun Turai, domin sau 6 ta na kaiwa wasan karshe a gasar sannan ta lashe gasar har sau uku.

Duk da cewa Inter bata nuna bajinta kamar yadda City ta yi ba a kakar wasan bana, amma kaiwa ga wannan da kungiyar tayi babban nasara ce a gare ta.

Simone Inzaghi

A bangaren mai horas da ita Inter Milan Simone Inzaghi, ya samu nasarar lashe dukkanin wasan karshen da ya buga a matsayin mai horaswa tun daga kungiyar Lazio da Inter Milan kuma kafin fara wasannin ba a ganin kungiyar da yake jagoran ta a matsayin wacce zata kai gaji.

Kamar yadda masu iya magana kance ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare, domin lokaci ne kadai zai tabbatar da kungiyar da zata yi nasara a wannan wasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.