Isa ga babban shafi

An sake zaftare wa Juventus maki

Juventus ta rasa maki 10 bayan wani sabon bincike da aka gudanar kan cinikin ‘yan wasa da kungiyar ta yi a baya.

Tambarin kulob din Juventus kenan
Tambarin kulob din Juventus kenan © goal
Talla

Tun da farko Juve ta fuskanci hukuncin da ya zabtare mata maki 15 a watan Janairu amma babbar kotun wasanni ta Italiya ta soke hukuncin a watan Afrilu tare da ba da umarnin sake duba lamarin.

An sanar da sabon hukuncin ne a ranar Litinin, kafin wasan da kungiyar za ta yi tattaki zuwa gidan Empoli.

Hukuncin dai ya kai ta matsayi na bakwai daga matsayi na hudu a saman teburin gasar Seria A, wanda hakan zai hana ta samun damar shiga gasar Turai.

Tuni dai Napoli ta samu nasarar lashe kofin Seria A, kuma kafin yanke hukuncin na ranar Litinin, tana gaban Juve da maki 17.

Mai gabatar da kara na tarayya Giuseppe Chiné ya nemi da a dakatar da jami’an kungiyar da ke da hannu a tuhumar na tsawon watanni takwas.

Hukuncin na nufin makin da Juve ke da shi zai koma 58, inda za ta kasance a matsayi na shida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.