Isa ga babban shafi

Hukumar Olympics ta goyi bayan haskawar 'yan wasan Rasha da Belarus a gasar

Shugaban hukumar shirya wasannin Olympics ta duniya,  Thomas Bach ya ce yadda wasu gwamnatoci ke sukar matakin dawowar ‘yan wasan motsa jiki na Rasha da Belarus fagen wasanni abin takaici ne. 

Paris ke shirin daukar nauyin gasar ta Olympics a shekarar 2024.
Paris ke shirin daukar nauyin gasar ta Olympics a shekarar 2024. © REUTERS / BENOIT TESSIER
Talla

Duk da matakin nuna kyama ga 'yan wasan kasashen biyu hukumar ta bayar da shawarar a kyale ‘yan wasa na Rasha da Belarus su shiga gasar amma ba a karkashin tutar kasashensu ba. 

Wannan na faruwa ne duk da cewa sama da kasashe 30 ke goyon bayan haramta wa ‘yan wasan wadannan kasashe shiga harkar kowanne nau'in wasanni. 

Bach ya ce irin wannan matsayi abin takaici ne, kuma ya na iya kawo karshen wasanni a duniya, lura da cewa tuni ya rage karsashin wasanni da dama. 

Nan gaba ne dai za a yanke hukunci ko ‘yan wasan na Rasha da Belarus za su shiga gasar Olympics ta shekarar 2024 wadda za ta gudana a birnin Paris na Faransa ko akasin haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.