Isa ga babban shafi
China

A yau ake bude gasar wasannin Olympics a birnin Beijin

A yau juma’a 4 ga watan fabrairu ne birnin Pekin na kasar China, ke buda soma wasannin motsa jikin  Olympique na hunturu,  birnin da kuma ya shiga tarihi a cikin wani irin yanayi mai nauyi sakamakon yaki da annobar corona, da kuma tada jijiyoyin wuyan diflomasiya da kasar ke yi da manayan kasashen duniya.

AP - Jae C. Hong
Talla

Kamar dai a 2008 musaman a filin wasan kasa  na Pékin, da ake yi wa lakabi da gijen tsuntsu ne,  za a buda soma gasar ta bana, da misalin karfe 8 na dare a gogon china 1 agogon GMT.

Kamar dai a shekaru 14 da suka gabata mai shirya fina-finan nan ne Zhang Yimou ke jagorantar shagulgulan buda gasar. Wanda a shekara 2008 ya shirya shagulgulan da suka dauke numfashin duniya  saboda  tsaruwa da ban sha’awa, inda ya yi amfani da  maraya dubu 14, a karkashin barbadin harken wutar kawa mai ban sha’awa .

Ba tare da mamaki ba a yau, Zhang Yimou ya yi alkawalin gudanar da shagulgulan da za su banbanta da wadanda ya taba gabatarwa, tare da la’akari da yanayin tsananin sanyin hunturu da ake ciki, na kasa da digo (-6°C) na ma’aunin sanyi,  ga kuma tada jijiyoyin wuyan diflomasiya, inda  zai yi amfanin yan wasa dubu  3 akasarinsu yara wajen shirya shagulgulan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.