Isa ga babban shafi

Sporting Lisbon ta fidda Arsenal daga Gasar Europa

An kammala zagayen ‘yan 16 na gasar Europa, inda a yanzu kungiyoyi 8 suka samu damar tsallakawa zagayen dab da na kusa da na karshe a gasar. 

'Yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Sporting Lisbon.
'Yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Sporting Lisbon. © AFP - PATRICIA DE MELO MOREIRA
Talla

Kungiyoyin da suka kai wannan mataki sun hada da Sporting Lisbon da Feyenoord da Juventus da Manchester United da Roma da Sevilla da Union Saint-Gilloise sai kuma Bayer Leverkusen. 

 Arsenal da aka saran zata tabuka abin azo a gani a gasar ta bana, ganin irin tagomashin da take samu wajen jagorantar gasar Frimiyar Ingila, Sporting Lisbon ta fidda ita daga gasar a bugun daga kai sai me tsaron gida. 

 A yau ne za’a hada yadda kungiyoyin za su hadu a matakin dab da na ku sa da na karshe da kuma zagayen kusa da na karshen na gasar.

 A ranar 13 ga watan gobe ne kuma za’a yi karawa tafarko na zagayen, sannan a buga karawa ta biyu a ranar 20 dukdai a watan na goben 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.