Isa ga babban shafi

Mu na da kwarin gwiwar lashe Gasar Zakarun Turai-Ancelotti

Mai horas da kungiyar Real Madrid Carlo Ancelotti ya ce ya na da kwarin gwiwar cewar kungiyar ta sa za ta kare kambun ta na gasar zakarun Turai, bayan da ta tsallaka zagayen dab da na kusa da na karshe a gasar. 

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Carlo Ancelotti.
Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Carlo Ancelotti. Reuters/Michaela Rehle
Talla

Zakarun gasar har sau14, sun lallasa Liverpool da suka buga wasan karshe a gasar shekarar da ta gabata da kwallaye 6 da 2 a karawa biyu da sukayi, bayan nasarar jefa kwallo daya tilo da Karim Benzema yyi a karawar su ta jiya a Santiago Bernabeu. 

Madrid na neman lashe gasar karo na 6 a cikin shekara 10, kuma Ancelotti ya ce kungiyar na da karfin gwiwar lashe gasa rkamar yadda ta yi a kakar bara.  

A bara kungiyar ce ta kakkabe kungiyoyin PSG da Chelsea da Manchester City kafin buga wasan karshe da Liverpool. 

A yanzu kungiyoyi 8 da sukayisaura a gasarsun hada da Chelsea da Benfica AC Milan da Bayern Munich da Manchester City da Inter Milan da Real Madrid sai kuma Napoli. 

A gobeJuma’a a birnin Nyon na Switzerlandza’a hada yadda kungiyoyin za su hadu da juna. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.