Isa ga babban shafi

Za mu yi amfani da dukkanin karfinmu don murkushe Liverpool- Ancelotti

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Carlo Ancelotti ya bayyana cewa za su yi amfani da dukkanin karfinsu wajen karasa murkushe Liverpool yayin haduwarsu ta gobe laraba, domin kuwa a cewarsa za su yi amfani da salon kai farmaki ne ba wai kare kai ba a wasan wanda ke matsayin zagaye na 2 a rukunin gab da na kusa da karshe karkashin gasar cin kofin zakarun Turai.

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Carlo Ancelotti.
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Carlo Ancelotti. REUTERS/Charles Platiau/File Photo
Talla

Ancelotti wanda ke wannan batu yayin amsa tambaya kan shirin da Madrid ta yi don kare kofin na ta,  ya ce duk da gagarumar tazarar da ke tsakanin Madrid da Liverpool ba za su saurarawa tawagar ta Jurgen Klopp a wasan na gobe ba.

Real Madrid wadda ke rike da kofin na zakarun Turai, ta yiwa Liverpool ruwan kwallaye ne a haduwarsu ta watan jiya inda aka tashi wasa 5 da 2 a Anfield bayan kwallaye bibbiyun da Karim Benzema da kuma Vinicius Junior suka zura a bangare guda kuma Eder Militao ya zura guda.

Lura da tazarar kungiyoyin biyu dai, Liverpool na bukatar akalla kwallaye 3 da nema gabanin iya tsallakewa zuwa matakin gasar na gaba, wanda kuma ake ganin abu ne mai wuya lura da rashin karsashin da tawagar ta Jurgen Klopp ke nunawa a wannan kaka.

Idan har Madrid ta fitar yi nasara kan Liverpool a wasan na gobe, hakan na nuna cewa sau 3 Madrid na yin waje da Liverpool a gasar ta cin kofin zakarun Turai ciki har da wasan karshe sau 2.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.