Isa ga babban shafi

Madrid ta sake haduwa da Chelsea a Gasar Zakarun Turai

An sake hada kungiyar Real Madrid da ke kare kambin gasar Zakarun Turai da Chelsea a wasan zagayen dab da na kusa da na karshe.

Tambarin hukumar shirya gasar zakarun Turai ta UEFA kenan
Tambarin hukumar shirya gasar zakarun Turai ta UEFA kenan © UEFA
Talla

A kakar da ta gabata, kungiyoyin sun hadu a irin wannan matakin inda Real Madrid ta samu nasara akan Chelsea.

Tawagar Pep Guardiola ta Manchester City za ta hadu ne da tsohuwar kungiyar sa Bayern Munich.

Sauran wasannin su ne, Napoli za ta hadu da AC Milan sai kuma Inter Milan ta barje gumi da Benfica.

Kungiyar da ta samu nasara tsakanin Real Madrid ko Chelsea za ta hadu da wadda ta samu nasara tsakanin Man City ko Bayern Munich, ya yin da a dayan bangaren zakara tsakanin Inter Milian da Benfica zai hadu da AC Milan ko kuma Napoli.

A ranar 11 ga watan gobe ne za’a duga wasan farko tsakanin Real Madrid da Chelsea sannan a ranar 12 ga watan City za ta karbi bakuncin Bayern.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.