Isa ga babban shafi

Courtois ya kafa tarihi a Qatar bayan nasarar Belgium kan Canada

Tawagar kwallon kafar kasar Belgium ta yi aiki tukuru wajen kare martabarta, inda ta ci Canada kwallo 1 mai ban haushi, ta kuma rike wasan a haka har aka tashi a wasan gasar cin kofin duniya da suka fafata a jiya Laraba.

Mai tsaron ragar Belgium, Thibaut Courtois.
Mai tsaron ragar Belgium, Thibaut Courtois. REUTERS/Sergio Perez
Talla

Canada ce ta mamaye akasarin wasan na rukunin F, sai dai ta yi ta baras da damarmakin saka kwallaye a raga, musamman a lokacin da ta samu bugun daga kai sai mai tsaron raga, Alphonso Davies ya buga amma mai tsaron raga Thibaut Courtois ya hana ta shiga. 

Yayin wasan na jiya Courtois ya kafa tarihin iya tare bugun fenariti a cikin wasa karkashin gasar ta cin kofin Duniya wanda rabon da ayi irin haka tun shekarar 1966 lokacin da ingila ta lashe gasar, wanda ke nuna cewa a cikin shekarar nan kadai mai tsaron ragar ya yi nasarar tare fenariti har 5 cikin 9 da aka buga masa.

Haka zalika Courtois ne mai tsraon raga daya tilo da ya halarci gasar cin kofin Duniya har sau 3 a jere, wato a shekarar 2014 da 2018 da kuma yanzu 2022.

Courtois ya kuma tare kwallon da Alistair Johnston ya kusan saka masa a raga, kuma bayan haka ne Belgium ta samu dama, inda Michy Batshuayi ya karbi wata kwallo daga Toby Alderweireld, ya kuma antaya ta a ragar mai tsaron ragar Canada Milan Borjan. 

Jonathan David shi ma ya baras da wata damar saka kwallo a ragar Belgium, kana Courtois ya ture wata kwallo da Cyle Larin ya kusan cin sa da ita.

Canada ta ci gaba da matsa wa Belgium lamba a zubi na biyu na wasan, amma hakarta ba ta cimma ruwa ba, duk kuwa da cewa ‘yan wasan Belgium ba su yi wasa dai dai da matsayinsu a duniyar kwallon kafa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.