Isa ga babban shafi

Qatar 2022: Netherlands ta lallasa Senegal a gasar cin kofin duniya

Kwallaye biyu da aka zura dab da za a tashi a wasa, sun baiwa Netherlands nasara da ci 2-0 a kan zakarun Afirka Senegal a ranar Litinin, yayin da 'yan wasan Louis van Gaal suka fara buga gasar cin kofin duniya a Qatar da kafar dama.

Senegal ta gaza samun nasara a wasanta na farko na rukuni
Senegal ta gaza samun nasara a wasanta na farko na rukuni AP - Ebrahim Noroozi
Talla

An zura kwallon farko a wasan ne cikin minti na 84 da farawa a rukunin A lokacin da dan wasan gaba Cody Gakpo ya jefa kwallon farko a ragar Senegal, kafin daga baya Davy Klaassen ya ci ta biyu a karawar.

Yayin da Senegal ta rasa tauraron dan wasanta a wasan, sakamakon rauni wato Sadio Mane, karawar da kasashen da ke rukunin A suka yi a farkon wasan an yi hasashen za a tashi kunnen doki babu ci.

Sai dai ana saura minti shida, dan wasan gaban PSV Eindhoven Gakpo ya yi dirar mikiya a gaban golan Senegal Edouard Mendy.

Sakamakon ya sa Netherlands ta zama ta daya a rukunin da Ecuador, wacce ta doke Qatar da ci 2-0 a wasan farko na ranar Lahadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.